1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayaka sun halaka sojojin Burkina Faso

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2022

Rahotanni daga Ougadugou babban birnin kasar Burkina Faso na cewa kimanin dakarun gwamnati bakwai ne suka mutu, bayan wasu tagwayen hare-haren mayakan jihadi a barikin soja.

Symbolbild Burkina Faso  Mehr als 138 Tote bei Anschlag
Hoto: Michel Cattani/AFP

Rundunar sojojin kasar ta Burkina Faso ta ce hari na biyu ya halaka farar hula daya, tare da jikkata wasu da dama da ke cikin motar fasinja. Harin ya faru ne bayan wani makamancinsa da ya kashe kusan  mutane 40 a ranar Asabar din da ta gaabata. Yawancin wadanda harin ya rutsa da su dai, fararen hula ne masu aikin sa kai tare da sojoji.

Burkina Faso dai ta sha fama da hare-haren masu jihadi tun shekara ta 2015, tare da yunkurin da ke da alaka da Al-Qa'eda da kungiyar IS. Sama da mutane 2,000 ne aka kashe, yayin da wasu miliyan daya da dubu 800 suka rasa muhallansu. Sabon shugaban kasar Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba dai, ya yi alkawwarin bai wa matsalar tsaro fifiko.