1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana yada labarai kan tsaro a Burkina

Gazali Abdou Tasawa
June 22, 2019

Majalisar dokokin Burkina Faso ta amince da wata sabuwar doka wacce ta tanadi hukuncin zaman kaso na shekaru goma ga duk wani da aka samu da laifin ba da labari kan ayyukan sojin kasar a fagen daga. 

Afrika Burkina Faso  l Militär - Kameruner Soldaten
Hoto: DW/F. Muvunyi

Dokar ta tanadi hukunta duk mutumin da ya wallafa wasu hotuna ko bidiyo na hare-haren da sojojin kasar suke fuskanta daga 'yan ta'adda, ko na mutanen da harin ta'addanci ya ritsa da su, ko kuma duk wasu hotuna ko bidiyo da ka iya taimakawa wajen sanyaya gwiwar sojojin kasar da ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Gwamnatin Burkina Faso ta ce burin da take son cimma a cikin wannan doka shi ne sa ido kan labaran da ake yadawa domin kauce yi wa kungiyoyin 'yan ta'adda farfaganda. 

Sai dai 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa sun fice daga zauren majalisar kafin soma muhawarar, suna masu zargin cewa gwamnatin ba ta yi wa jama'a cikakken bayani kan dokar ba. Suma dai kungiyoyin 'yan jarida na kasar ta Burkina Faso sun soki lamirin dokar wacce suka bayyana a matsayin tauyin 'yancin aikin jarida a kasar.