1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso, amincewa da ranar zabe

November 6, 2014

Masu ruwa da tsaki a kasar Burkina Faso sun amince da ranar gudanar da babban zabe da zai mayar da kasar kan turbar dimokaradiyya.

Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Rahotanni sun bayyana cewa masu ruwa da tsakin da suka hadar da 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula da kuma sojojin kasar sun amince a yi zabukan kasar cikin watan Nuwamban shekara mai zuwa ta 2015. Sun dai cimma wannan matsaya ne yayin zaman da suka yi a Wagadugu babban birnin kasar a Alhamis din nan. Taron dai ya samu halartar shugabannin kasashen nahiyar Afirka guda uku ciki kuwa har da Shugaba Good Luck Jonathan na Najeriya tare kuma da shugabnnin adinai da sarakunan gargajiyar kasar. Burkina Faso dai ta fada cikin tasku ne bayan da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ya nemi yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar domin ya samu damar yin tazarce, batun da al'ummar kasar suka ce basu yadda ba, wanda kuma ya kai ga tilasta masa yin murabus.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu