Farkamin soja ya kashe 'yan ta'adda 30 Burkina
February 24, 2019Talla
Rahotanni sun ce rundunonin sojan kundunbala, hadin gwiwa da na sojan sama ne suka kai kai samamen a yankunan da ke a matsayin maboyar mayakan na jihadi.
Tuni ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso ta bayyana cewa, ko baya ga hallaka mayakan jihadin, rundunar sojan kasar ta yi nasarar kwato makamai da dama tare lalata tarin abinci.
Shekaru hudu kenan da Burkina Faso ke fama ne da matsalolin tsaro musamman ma hare-haren ta'addanci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami'an tsaron kasar.