1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya hallaka mutane a Burkina Faso

Binta Aliyu Zurmi
March 14, 2021

Rahotanni daga Ouagadougou na kasar Burkina Faso na cewar wasu tagwayen hare-haren ta'addanci sun yi sanadiyar mutuwar mutum uku ciki har da jami'in 'yan sanda daya.

Burkina Faso Franzöische Soldaten Operation Barkhane
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Wannan harin shi ne ke zama na baya-bayan nan da kasar ke fuskanta, a cewar binciken da aka gudanar maharan sun isa garin Batie ne a kan babura, haka zalika a rana guda a wani kauye an kai hari a kan masu ayyukan agaji da ke taimakawa soji a yakin da suke yi da 'yan ta'addan.

Ko a satin da ya gabata an sami asarar rayukan mutum 6 a yayin wani harin kwanton bauna a sansanin sojoji da ke arewacin kasar.

Yanzu haka ana sa ran isar sama da dakarun soji  dubu daga kasar Chadi domin taimaka kara tsaro a kan iyakokin kasar da Mali da Nijar.