1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ce kutal da 'yan gudun hijira ke sha wuya

Abdullahi Tanko Bala
June 3, 2024

Kungiyoyin agaji sun yi gargadi kan wahalhalu da rashin kwanciyar hankali da 'yan gudun hijirar da aka manta da su suke ciki a Afirka.

Wasu 'yan gudun hijirar Burkina Faso da Sudan
Wasu 'yan gudun hijirar Burkina Faso da SudanHoto: Michael Kappeler/picture alliance/dpa

Majalisar kula da yan gudun hijira ta kasar Norway a rahotonta na shekara da ta wallafa a yau Litinin ta zayyana kasashe goma a yammaci da tsakiyar Afirka inda ta ce an manta da 'yan gudun hijira da ke cikin mawuyacin hali.

Kasashen sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Mali da Nijar da Honduras da Sudan ta Kudu.

Sauran sun hada da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Chadi da kuma Sudan.

A watan Afrilun da ya gabata, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yan gudun hijira fiye da miliyan goma sha biyu suka tagaiyara a yankin yammacin Afirka da kuma Afrika ta tsakiya.

Sojoji da ke mulki a Burkina Faso su na fama da boren masu ikrarin jihadi. A shekarar 2023 mutane fiye da 8,000 suka rasa rayukansu a tashe tashen hankula.