1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Cibiyar matasa masu hazakar kwamfuta a birane

Gerlind Vollmer/ KSNovember 11, 2015

Gildas Guiella ya cika burinsa. Shi da wasu injiniyoyin kwamfuta 11 sun kafa kamfanin fasahar kere-kere na farko a kasashen Afirka rainon Faransa da suka sa wa suna OuagaLab.

Start up Burkina Faso Gildas Guiella
Hoto: DW/G. Vollmer

Kasancewar dakin harhada naura mai kwakawalwa na farko a kasashen Afrika rainon Faransa ba wani abu ne mai sauki ba.

Wasu gungun matasa da ke da masaniyar harkar naura mai kwakwalwa a kasar Burkina Faso ne a inda suka samar da wata kungiya don tallafa wa matasan nakaltar harkokin fasahar zamani.

Gildas Guiella na daya daga cikin wadanda suka kafa dakin harhada karikitan naura mai kwakwalwa da ake kira da suna OuagaLab, wanda tutar kasar ke kadawa a gaban farfajiyar ginin. Yanzu haka dai matasan sun sami nasarar tara wa cibiyar tasu kudaden cigaba da harkokinsu kamar yadda ya kamata, kuma yanzu matasan sun fito gadan-gadan don tallata kansu. Gildas Guiella na mai cewar:

"Ya zama wajibi na bayyana cewar mutane ba su san cewar muna nan a Ouagadougou ba sabili da dadalin "Website" dinmu mutane masu tarin yawa a kasashen ketare sun san da zamanmu, musamman a Turai. To amma yanzu muna aiki tukuru domin sauya hakan wajen samar da dakin kera kayayyaki mai suna OuagaLab."

Matattarar matasa masana ilimin komfuta

Dakin harhada kayayakin na'ura mai kwakwalwa guri ne da ke kunshe da ma'aikata da ke aikin harhada wayoyi don samar da duk wani abu mai aiki da da wayoyi.

Hoto: Reuters

Wata na'urar yin printin takardu mai sunan D-3 wanda Gildas Guiella ya ciwo a yayin gasar na'ura mai kwakwalwa da aka yi a kasar Faransa. Wannan kua abin jin dadi ne, abin kuma alfahari a gare shi. Yanzu haka suna fatan yin kasuwanci da ita tare da wani masanin harhada na'urori na karkara inji Gildas Guiella.

"Wadannan masu fasahar da ke a karkara ba su taba ganin na'urar Printer D-3 ba ko kuma yadda take aiki ba, to amma suna da 'yar masaniyar yadda 3-D Printer take gami da yadda za ayi da ita."

Atsou Adote daya ne daga cikinsu cewa ya yi.

"Ina ganin cewar da samun irin su na'urar yin printing ba da jimawa ba ne za ka iya samar da irin su ko wasu bangarorinta."

Tallafa wa yara manyan gobe

Tayin aiki na keke da keke wajen samar da amsar matsalolin harkokin kasuwancin karkarar. Dakin harhada kayayyakin na'urorin sun tsunduma gadan-gadan wajen samar da na'urori masu kwakwalwa ga yaran makarantun Firamare. A wannan karon kamar ko da yaushe Gildas Guiella na ziyarar wani aji ne kunshe da dalibai.

"Mun zo ne nan domin mu fahimci irin yadda kuka gane nakaltar na'ura mai kwakwalwa. Wasu daga cikin ku da tuni suka fahimci yadda take, za su kara fahimtarta kana kuma wadanda ba su da iliminta za su fahimci sabuwar duniya daga yau."

Mafi yawancin yaran dai ba su taba ganin na'ura mai kwakwalwa ba a don haka suna cike da zumudin yadda Gildas Guiella zai nuna musu.

"Muna son bai wa duk wani yaro damar nakaltar ilimin na'ura mai kwakwalwa ne tun da fari kafin ya zamo babba. Muna yin amfani da dakin harhada na'urorinmu don sada bayanan ga yaran."

Muddin dai abubuwa suka tafi kamar yadda Gildas Guiella suka tsara, to shakka babu makarantun Firamare za su sami tasu na'urar mai kwakwalwa.