1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso da Mali da Nijar sun fice daga kotun duniya

September 23, 2025

Kasashen da ke karkakashin ikon sojoji sun fada a hukamance cewa sun raba gari da kotun duniya, saboda abin da suka kira rashin adalci da ake nuna wa wasu kasashen da ke cikin yarjejeniyar kafa kotun.

Shugabannin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso
Shugabannin kasashen Mali da Nijar da Burkina FasoHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Kasashen yammacin Afirka da sojoji ke mulki a cikinsu wato da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar, sun sanar da ficewarsu daga Kotun Duniya (ICC), tare da kiran kotun a matsayin kayan aikin danniya na "sabon mulkin mallaka” a hannun manyan kasashe.

Shugabannin sojan kasashen uku da suka kafa kawance (AES), sun ce kotun ta nuna gazawarta wajen magance manyan laifuka irin su yaki da take hakkin bil Adama da kuma kisan kiyashi.

Kasashen sun kuma bayyana aniyarsu ta kafa hanyoyin gargajiya don karfafa zaman lafiya da adalci a yankin.

Kotun ICC, mai hedikwata a birnin The Hague na kasar Holland, wacce aka kafa a shekarar 2002, ta kafu ne domin gurfanar da wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka musamman na yaki – a lokutan da kasashe suka kasa ko kuma ba su da niyyar yin hakan da kansu.