1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Dakile yunkurin tada zaune tsaye

January 19, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta yi ikirarin cewa ta dakile wani yunkuri na tada zaune tsaye tare da kaddamar da farautar wani gungun mutane da suka hadar da sojoji da fararen hula.

Gwamnatin Burkina Faso ta dakile yunkurin tada zaune tsaye
Gwamnatin Burkina Faso ta dakile yunkurin tada zaune tsaye Hoto: AA/picture alliance

A cikin wata sanar da aka wallafa, ministan sadarwar Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo, ya ce tun a ranar 13 ga watan Janairu jami'an tsaron kasar ke aiki tukuru domin wargaza wannan gungu da ake zargi da neman mayar da hannu agogo baya tare da kawo cikas ga tsarin sake gina kasar da dawo da mutumcinta da kuma diyauci. Sanarwar ta kuma kara da cewa gungun da ya kunshi sojoji da fararen hula da ke kuma samun goyon baya daga wata kasar waje ya tuntubi mutane da dama a barikokin soji daban-daban domin tayar da kayar baya da nufin cimma wata manufa.

Karin bayani: An dakile yunkurin juyin mulki a burkina Faso

A baya-bayan nan dai an yawaita yin garguwa da manyan jami'an gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso, ciki har da tsohon babban hafsan hafsoshin jami'an Jandarma Kanal Evrard Somba, wanda wadansu murane dauke da makamai suka sace a gidansa da ke Ouagadougou kamar yadda makusantasa suka tabbatar.