1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Damuwa kan kashe fararen hula

Suleiman Babayo AH
May 31, 2024

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan kashe-kashe fararen hula a kasar Burkina Faso daga bangaren jami'an tsaro masu neman dakile 'yan ta'adda,

Burkina Faso | sojoji
Sojojin Burkina FasoHoto: Kilaye Bationo/AP Photo/picture alliance

Babban jami'in kula da kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya bayyana damuwa kan kara samun kashe-kashen fararen hula a yankunan kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka. Babban jami'in ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Jumma'a, inda ya bukaci cikekken bincike kan abin da yake faruwa a kasar.

Ita dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa jami'an tsaron ta Burkina Faso da masu mara musu baya suna halaka fararen hula da dama da suke zargi da hannu cikin tashe-tahsen hankula da kasar take fuskanta.