1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Burkina Faso na daukar sabon salo

Kamaluddeen Sani/ YBSeptember 21, 2015

Rahotanni na nuni da cewar tuni wasu manya-manya a rundunar sojojin kasar Burkina Faso suka hallara a Ouagadougou domin kwance wa masu tsaron fadar shugaban kasa damara.

Burkina Faso Ouagadougou General Gilbert Diendere
Janar Gilbert Diendere da ya kwaci mulki a Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Wannan mataki na zuwa ne bayan wata zanga-zanga da ta barke akan titunan babban birnin kasar.

Tun dai bayan kifar da gwamnatin kasar Burkina Faso da wasu sojojin kasar suka yi a makon da ya gabata, kasashen duniya da ma kungiyoyin kasa da kasa ke ta kururuwar ganin an saisaita harkokin mulkin dimokaradiya a kasar tare da yin Allah wadai kan yadda sojojin suka maido da hannun agogo baya ganin watan gobe ne ya yi saura kasar ta gudanar da zaben shugaban kasa da sauran zabubbuka a duk fadin kasar.

Duk da dai yunkurin da Shugabanin kungiyar habaka harkokin tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS ke yi kan warware rikicin kasar har yanzu masu zanga-zanga na ci gaba da kasancewa a kan titunan birnin kasar a inda suke kone-kone tare da shingice hanyoyi domin nuna adawar su ga batun duk wani shiri da zai kai ga bai wa na hannun daman tsohon shugaban kasar kaiwa ga madafun iko.

Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojaHoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

Masu zanga-zangar dai suna masu cewar "Ku fice daga taron bama bukatar ku muna kira ga Faransa da Amirka su kawo dauki, mutum daya ba zai jefa kasar cikin mawuyacin hali ba".

Shi kuwa Jean Paul mutumin da harsashi ya samu abokinsa Badama Bazie yayin zanga-zangar cewa yake.

Sojoji na sintiri a birnin OuagadougouHoto: Reuters/J. Penney

"Muna zaune sai muka ga harshashi ya biyo ta bayan mu ya keta ta cikin bishiyoyi ya sami abokin zamana daga nan ne yake gaya mana cewar harbin bundiga ne haka dai muka rasa shi ba tare da fahimatar komai ba".

Tuni dai manya-manyan jagororin rundunar sojojin kasar suka ce masu gadin shugaban kasar da suka kifar da gwamnati su mika makamansu to sai dai kuma a hannu daya Shugaban kasar Faransa Farancois Holland ya yi gargi da cewar yin watsi da yarjejeniyar da kungiyar ta ECOWAS ta ke shiga tsakani ka iya janyo fushin hukumomin kasar ta Faransa ga mahukuntan kasar Barkina Faso.

Yanzu haka dai kungiyar ECOWAS ta cikin shirin yarjejeniyar cimma dai daiton siyasar Barkina Faso sun sanya ranar 22 ga watan Nuwamba a kalla domin gudanar da zaben shugaban kasar da na majalisun dokokin kasar gami da janye haramcin da aka sanya wa na hannun daman Blaise Compore kan shiga zaben.