1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana hawa babura a Burkina Faso

June 10, 2021

Hukumomi a Burkina Faso sun zartas da hukuncin haramtawa babura yin zirga-zirga a yankunan arewacin kasar, har sai abin da hali ya yi.

Tschad I Dorf Bélégramme im Departement Kabia
'Yan ta'adda kan yi amfani da babura wajen kai hare-hare Hoto: Blaise Dariustone/DW

Wasu manazarta dai na ganin matakin hana hawa baburan da gwamnatin Burkina Fason ta dauka, ba zai magance matsalar tsaro da kasar ke fama da shi ba. Halin da kasar ta Burkina Faso ta samu kanta a ciki a baya-baya nan na hare-hare mafi muni da ba ta taba fuskanta ba, na cikin daililan da ya sa gwamnatin ta dauki wannan mataki na haramtawa babura zirga-zirga kasancewar mafi akasari 'yan ta'addar a kan baburara suke kai hari. A hari na baya-bayan nan ma, mutane kusan 160 da suka hadar da maza da mata da yara ne suka halaka a Solhan da ke Arewo maso Kudancin kasar.

Karin Bayani: Yawaitar yunwa a Sahel saboda ta'addanci

A Burkin Faso dai babur ko keke, na da muhimmanci ga al ummar kasar da suke yin amfani da shi don zirga-zirgarsu ta yau da kullum a birane da kauyuka, a cewar Idris Birba shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Burkina NDH: "Haramta ababen hawa masu kafa biyu moto ko basukur a inda jama'a ke yin ta'ammali da su wajen yin kasuwnci da harkokinsu na yau da gobe, wata hanya ce ta hana mutane samun ababen rayuwa. Abin da yakamata shi ne, a samar da sojojin da suka dace da kuma kayan aiki. Gaskiya ne sojoji na yin sintiri a yankin, amma kuma idan sun kammala sukan fice."

Hare-hare na kara kamari a kasashen yankin Sahel da Tafkin ChadiHoto: Str/AFP

Akwai da wahala ga sojojin su iya kula da abin da ke faruwa, hasali ma ta yadda 'yan taddar ke hada baki da jama'ar gari. Amadou Harouna Maiga shugaban wata kungiya da ke fafutuka a Tilaberi a yammacin kasar, inda ake fama da hare haren 'yan ta'adda, ya ce an dauki matakin haramta amfani da babura a Mali da Jamhuriyar Nijar amma har yanzu babu saukin hare-haren: "An haramta babuburan amma dukkanin hare-haren da ake kai wa a yankin Tilaberi da babura ake kai su. Sojoji suna la'akari da wadanda ke zirga-zirga a kan mashin din ne. Suna da jama'ar da ke cikin gari da suke sanar da su abin da ke faruwa."

Karin Bayani: Muhawara ta barke a kan batun tsaro a Najeriya

Yankin arewacin Najeriya dai, ya kasance n farko wajen daukar irin wannan mataki kafin Jamhuriyar Nijar da Mali a kokarin da ake na samun zaman lafiya. Sai dai a ganin Musa Tchangari shugaban kungiyar Alternative da ke Nijar, kwanciyar hankali ba za ta taba tabbata ba sai da adalci. Bayan haramta babura zirga-zirga a Burkina Fason dai, hukumomin kasar sun kuma rufe ciboyoyin hako zinari na gargajiya a yankin arewacin kasar tare da kafa dokar hana fita da daddare daga karfe bakwai na yamma har karfe biyar na safe.