Mutane 27 sun mutu a harin 'yan ta'adda
July 4, 2022Talla
Maharan da ake kyautata zaton masu da'awar jihadi ne sun hallaka fararen hula 27 ciki har da mata da kananan yara a wasu yankunan Bourasso da Yatenga da ke Arewa maso yammacin Burkina Faso.
Wata majiyar tsaron ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa maharan sun yi harbi irin na kan mai uwa da wabi a garuruwan.
Tun a shekarar 2015 kasar Burkina Faso ke fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu alaka da Jihadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane baya ga wasu kusan miliyan biyu da suka tsere daga gidajensu.
A yanzu Burkina Faso mai makwabtaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ta rasa fiye da kaso 40 cikin dari na kasarta inda ya fada hannun kungiyoyi masu tayar da kayar baya.