An kashe mahaka zinare a Burkina Faso
October 6, 2019Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wasu majiyoyin tsaro na kasar ta Burkina Faso na cewa maharan dauke da bindigogi sun kai harin ne a yamamcin ranar Juma'ar da ta gabata, inda suka bude wuta kan mahaka zinaren tare da halaka 20 kana wasau da dama suka jikkata.
A wannan yanki ne dama a tsakiyar watan Satumban da ya gabata, mayakan kungiyoyin da ke da'awar jihadi suka tarwatsa wata gada da ke kan hanyar biranen Djibo da Dori na arewacin kasar. A ranar Litinin din makon da ya gabata ma dai fararen hula tara ne suka halaka a cikin wasu jerin hare-hare da aka kai a garuruwan Pissele da Boulkiba na karamar hukumar Bourzanga ta jihar Bam a arewacin kasar, kana wasu mutane sama da 20 suka mutu a wasu jerin hare-haren a jihar ta Bam, lamarin da ya tilasta wa mutane sama da dubu 20 tserewa zuwa birnin Kongoussi.