Mayaka sun kashe 'yan sanda a Burkina Faso
June 10, 2022Wata majiya ta ce, "A daren ranar Alhamis ne 'yan ta'adda suka kai hari a wani sansanin Jandarma a Seytenga da ke lardin Seno." Majiyar ta kara da cewa "Kimanin jandarmomi 10 sun mutu, hudu sun samu raunuka, an kuma yi barna sosai,” akwai yuwar adadiny a karu inji majiyar.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da harin, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren zubar da jini a kasar Burkina Faso. Majiyar ta kara da cewa jami'an tsaro sun fatattaki maharan a wani hari da suka kai musu, inda a yanzu haka suke farfasa wurin.
"Har yanzu ba a ga wasu dakaru da dama ba" har zuwa safiyar Juma'a, in ji majiyar ta biyu. Daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, Burkina Faso ta fada cikin rikici na kusan shekaru bakwai da mayakan jihadi suka tsallaka daga makwabciyar kasar Mali.
Wannan harin dai ya faru ne bayan wani harin a jiya Alhamis ya kashe jami'an tsaro a yammacin lardin Kossi da wani hari a mahakar zinari a arewacin kasar.
Hare-haren 'yan ta'adda a Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 2,000, a yayin da kusan mutane miliyan 2 sun tsere wa gidajensu sakamakon ayyukan ta'addanci musamman a arewacin kasar.