Burkina Faso na cikin rudani
September 22, 2015Jagoran juyin mulkin soja a ƙasar Burkina Faso ya bayyana cewa har yanzu shi ke da iko da ƙasar a ranar Talatan nan duk kuwa da cewa ya tsallake lokacin da aka bawa rundinar sojan da suka jagorancin juyin mulki su kwance damara.Janar Gilbert Diendere da ya kwaci mulki a makon da ya gabata daga hannun gwamnatin riko ya bayyana cewa a shirye yake a shiga tattaunawa da shi amma yana jira ne ya ji makomar taron shugabannin kasashen Yammacin Afirka da ke gudana a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.
Janar Diendere a wani taron manema labarai ya bayyana cewa ba ya zo ya dawwama bane, zai rike madafun iko ne na dan wani lokaci. Kuma sojan da ke kare shi a shirye suke su maida martani duk wanda ya kai musu hari.
Mutane dai sun fantsama a tituna a birnin da cikar wa'adin ƙarfe goma da aka ba wa sojojin su kwance damara, inda su kuma sojoji da ke mara baya ga Janar Diendere suka kankane fadar shugaban kasa, wasu sojojin da ke adawa da shi kuma suka rike wasu manyan wurare cikin shirin ko ta kwana.