Burkina Faso: Makoma bayan juyin mulki
October 14, 2022Talla
Tattaunawar na zuwa ne makwanni biyu bayan da kasar ta yankin Sahel da ke fama da rikicin ta'addanci ta fuskanci juyin mulki a karo na biyu cikin kasa da watannin tara.
Yayin zaman tattaunawar, ana sa ran a nada wanda zai gaji hambararren shugaban mulkin sojin kasar Henry Damiba a matsayin shugaban rikon kwarya da zai shugabanci kasar kafin mayar da ita tafarkin dimokradiyya.
Shugaban kwamitin shirya taron Kanar Celestin Compaore, ya ce taron zai yi nazari tare da amincewa da yarjejeniyar mika mulki da kuma karbar duk wasu shawarwari don aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Kasar ta Burkina Faso ta sha fuskantar juyin mulki tun bayan samun 'yancin kai daga uwargijiyarta Faransa.