1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso: Ana yi wa gwamnati bore saboda rashin tsaro

June 27, 2021

A Burkina Faso dubban mutane sun yi zanga-zanga, inda suke neman gwamnati ta kara azama wurin kare su daga hare-haren masu ikirarin jihadi.

Roch Marc Christian Kabore gewinnt Wahl in Burkina Faso
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta sanar da samun galaba a kan 'yan ta'addan da ke kasar. 

Babbar zanga-zanga ta gudana jiya a birnin Kaya da ke zama shelkwatar yankin arewa na tsakiyar kasar ta Buirkina Faso, inda mutane suka rika nuna kwallayen da aka rubuta cewa ''mun gaji da tabarbarewar tsaro, muna son zama lafiya.'' 

Rahotanni sun ce an kuma gudanar da makamanciyar irin wannan zanga-zangar a wasu bangarori na kasar.

Mutane sama da 100 ne dai 'yan ta'addar Burkina Fason suka kashe a farkon wannan wata a wani mummunan hari da ya tayar da hankulan mutanen kasar. Sai dai zanga-zangar bukatar inganta tsaron, ta biyo bayan wata sanarwa da sojojin Burkina Faso hadin gwiwa da na Nijar suka bayar cewa sun halaka fiye da 'yan ta'adda 100 a Burkina Faso bayan wani samame na makonni biyu da suka kaddamar.