1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Sai tsaro ya inganta kafin a yi zabe

September 30, 2023

Shugaban majalisar mulkin soji a Burkina Faso, Ibrahim Traore ya ce babban abun da gwamnatin ta sanya a gaba shi ne tabbatar da tsaro ba gudanar da zabuka ba.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahim TraoreHoto: Alexey Danichev/AFP

Shugaban ya ce, ya na shirin kawo sauyi mai inganci a kundin tsarin mulkin kasar da ke kasancewa ra'ayin wasu tsurarun mutane ba na al'ummar kasar ba. Ko a farkon watan Satumba, Burkina Faso ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasashe Mali da Nijar da su ma ke karkashin mulkin soji.

Karin bayani: Traoré zai ci gaba da jan ragamar mulki

Traore ya ce, al'amuran tsaro sun fara inganta a kasar kana dakaru na samun nasara a fagen daga. A ranar Juma'a ne dai dubban magoya bayan mulkin soji suka yi gangamin a birnin Ouagadougou domin murnar cikar sojojin shekara guda da kwace mulki daga hannun farar hula.

Karin bayani: An fara kokarin kafa gwamnatin riko a Burkina Faso

A ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2022, shugaba Traore ya jagoranci juyin mulki da ke zama na biyu cikin watanni takwas a kasar. A baya dai shugaban ya yi alkawarin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya tare da gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yulin badi.