1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar da kawo karshen mulkin Shugaba Compaoré

Abdourahamane Hassane MNA
October 31, 2019

Shekaru biyar ke nan da dubun dubatan jama'a a Burkina Faso suka yi wani bore na juyin juya halin da ya kawo karshen mulkin Blaise Compaoré.

Blaise Compaore Ex-Präsident Burkina Faso
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Mori

A Burkina Faso shekaru biyar ke nan da dubun dubatan jama'a suka kaddamar da wani bore na juyin juya hali da ya kai ga hana Blaise Compaore canza kundin tsarin mulki domin ci gaba da darewa kan madafun iko. Abin da ya kawo karshen mulkinsa a ranar 31 ga watan Oktoba na shekara ta 2014. Sai dai shekarun biyar din bayan faduwar gwamnatin Compore al'amuran tsaro sun jagule a Burkina Faso galibi a yankin arewaci saboda yawan hare-hare na 'yan ta'adda.

Babu Shakka a yau Burkina Faso tana cikin wani hali na rashin tabbas tun bayan faduwar gwamnatin ta Blaise Compaore sakamakon yadda kasar ke fuskantar hare-hare na kungiyoyin 'yan ta'adda wanda kawo yanzu suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 600 fararan hula da kuma sojoji, kana suka tilasta wa wasu kusan dubu 500 ficewa daga matsugunansu.

Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Compaore wanda ya kwashe shekaru 27 a kan karagar mulki ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a kasar, ko da ma dai yana da nashi laifin. Tsakanin tsohon shugaban na Burkina Faso dai da masu yin jihadin akwai kusan yarjejeniya ta kauracewa kai hare-hare. Laurent Kibora kwarrare ne a kan sha'anin tsaro.

''Blaise Compaore a lokacin yana zama mai shiga tsakani wanda hakan ya samu yardar masu yin jihadin a yankin Sahel, kuma yana kewaye da masu ba shi shawara na gari wadanda suka san abin da ya kamata. Sannan a lokacin akwai wata runduna ta musamman da ake kira da sunan GIAT mai yaki da ta'addanci yanzu duk an rusa wadannan abubuwa.''

Blaise Compaore ya dade yana tare daga a kasarsa da ma sauran kasashen Sahel wanda ya sha shiga tsakani a rikicin masu jihadi da na 'yan tawaye a Nijar da Mali, wanda a yau dukkanin wadannan kasashe suke cikin hali na gaba kura baya siyaki sakamakon yadda daga dukkkanin yankunan kasashen ake fuskantar hare-hare na 'yan ta'adda.

Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Daya daga cikin kungiyoyi masu yin jihadin da ke yawan kai hare-hare a Burkina Faso ita ce ta Front de Liberation da Macina ta Amadou Koufa da kuma Al Mourabitoune ta Mokhtar Belmokhtar. Sannan ban da ma hare-haren na 'yan ta'adda rikicin kabilanci ya kara bazuwa tun bayan faduwar gwamnatin ta Blaise Compaore a cewar Siaka Coulbaly wani mai yin fashin baki.

"Wani karin rashin tsaro ne inda har ba a tanadi abubuwan da suka dace ba domin tabbatar da tsaro. Kuma ba ta da karfin iko a kan wasu yankunanta, hakan na iya sa kowa ya yi gaban kansa a cikin irin wannan rikici tsakanin kabilu."

A shekarar badi aka shirya za a yi zaben shugaban kasa a Burkina Faso, sai dai ana da fargabar yiwuwar yin zaben cikin kwanciyar hankali a game da barazanar da ake fuskanta ta 'yan ta'adda.