Burkina Faso: Dakatar da RFI a kasar
December 3, 2022Talla
Dakatar da kafar RFI a Burkina Faso na zuwa ne sakamakon tuhumar da ta yi wa kafar na yada labaran bogi da kuma ba 'yan ta'adda damar fadin albarkacin bakinsu.
A cikin sanarwar da gwamnatin sojin kasar ta fitar, ta ce ta dauki matakin ne na dakatar da kafar daga yada shirye-shirye a kasar sakamakon jawabin barazana ga al'umma na shugaban wata kungiyar 'yan ta'adda da kafar ta yada a wannan Asabar din.
Sanarwar ta kuma karyata rahoton kafar RFI wanda ya nuna cewa shugaban mulkin sojin kasar Kaptin Ibrahim Traore, wanda ya kwace ikon kasar a watan Satumbar da ya gabata ya yi ikirarin cewa wasu sun yi yunkurin yi masa juyin mulki. Har kawo yanzu, kafar yada labaran bata ce komai dangane da dakatarwar ba.