1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta kafa dokarar haramta dabi'ar neman jinsi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 2, 2025

Ministan shari'a na kasar ya ce duk wanda ya maimata laifin kuma ba shi da shaidar 'dan kasa to za a kore shi daga kasar

Ministan shari'a na Burkina Faso Edasso Rodrigue Bayala
Hoto: Alexei Danichev/SNA/IMAGO

Majalisar zartarwar Burkina Faso ta amince da dokar haramta dabi'ar neman maza a kasar, tare da yin tanadin hukuncin daurin shekaru 5 a kurkuku, ga duk wanda aka kama da aikata wannan laifi.

Ministan shari'a na kasar Edasso Rodrigue Bayala, ya ce hukuncin ka iya farawa daga daurin shekaru 2 a gidan yari da kuma tara, wanda ya sake maimata laifin alhalin ba shi da takardar izinin zama 'dan kasa, to zai fuskanci hukuncin kora daga kasar.

Karin bayani:Wasu kasashen AES sun kauce wa taron tsaro na Abuja

Wasu kasashen Afirka da suka kaddamar da irin wannan doka ta Burkina Faso, wadda ta haramta neman jinsi, sun hada da Senegal da Uganda da Malawi, sai Afirka ta Kudu da Botswana da kuma Angola.