SiyasaAfirka
Burkina Faso ta kori Jakadun Faransa
April 18, 2024Talla
Wannan dai wata alama ce da ke nuna ci gaba da tsamin dangantaka tsakanin Burkina Fason da kuma uwar gijiyarta Faransa.
A cikin wata sanarwa da Burkina Faso ta aike wa ofishin jakadancin Faransa a ranar Talata, ta bukaci mutanen uku su fice daga kasar cikin sa'o'i 48.
Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta ce mutanen su ne Gwenaelle Habouzit, Herve Fournier da kuma Guillaume Reisacher.
Ofishin harkokin wajen Faransa dai bai ce uffan ba a kan wannan batun kawo yanzu.
Tun bayan da ya karbe madafun iko ta hanyar juyin mulki a watan Satumban 2022, shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Captain Ibrahim Traore ya ci gaba da nesanta kasarsa da Faransa wacce ta mulki Burkina Fason tun a shekarar 1960.