Burkina Faso ta rufe shafin DW kan kwarmata kisan kiyashi
April 29, 2024![Tambarin Deutsche Welle](https://static.dw.com/image/60687616_800.webp)
Dama kungiyar Human Rights Watch ta yi zargin sojoji da halaka mutane sakamakon taimaka wa masu ikrarin jihadi da ke dauke da makamai.
Karin bayani: Burkina Faso ta yi fatali da zarge-zargen Human Rights Watch
Sai dai hukumomin kasashen Amurka da Burtaniya sun nuna damuwa dangane da kisan na fararen hula da ake zargin sojojin kasar da aikatawa, a wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen biyu suka fitar.
Karin bayani: Ana zargin sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula 223
Hukumomin Burkina Faso sun dakatar da ayyukan kafafen yada labaran kasashen ketare a kasar ciki har da shafin Internet na Deutsche Welle na kasar Jamus da jaridun Faransa da suka hadar da Le Monde da Ouest-France, har ma da jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya da kuma wasu kamfanin dillancin labarai na Afirka.