Burkina Faso ta yanke wa wasu mutane 13 hukuncin kisa
August 12, 2025
Kotun ta Burkina Faso ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 zuwa 21 ga wasu mutanen akalla 60, wadanda ke da hannu a tada zaune tsaye da kuma kai harin ta'addanci hedikwatar sojojin birnin Ouagadougou da kuma ofishin jakadancin Faransa ta hanyar amfani da bindigogi da kuma tada bam a cikin mota.
Karin bayani: Gwamnatin Burkina Faso ta rufe fitaccen gidan rediyon kasar
Tashe-tashen hankula a kasar Burkina Faso ya halaka mutane sama da dubu 26,000 tun daga shekara ta 2015, ciki har da sojoji da fararen hula.
Karin bayani: An yi zanga-zangar goyon bayan sojojin da ke mulkin Burkina Faso
Rahoton kungiyar da ke tattara kididddigar mutanen da suka mutu a kasar ta ACLED ta ce rabin wadanda suka mutu sun rasa rayukansu ne a lokacin gwamnati mai ci ta Kyaftin Ibrahim Traore duk da yunkurin da yake yi na tabbatar da tsaro.