1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso: Zaman makoki bayan harin ta'addanci

Mouhamadou Awal Balarabe
August 26, 2024

Fararen hula fiye da 100 ne suka mutu a harin daga cikin sama da matasa da tsofaffi 600 da suka yi gangami domin tona ramuka don dakile hare haren yan ta'adda.

Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore
Shugaban Burkina Faso Ibrahim TraoreHoto: Donat Sorokin/TASS/dpa/picture alliance

Wadanda harin ta'addancin ya ritsa da su na taimaka wa sojojin Burkina Faso haka ramuka ne domin dakile yunkurin farmaki na kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai. 

Karin Bayani: An kashe gomman mutane a Burkina Faso

A halin da ake ciki dai, al'ummar Burkina Faso na cikin damuwa saboda hare-haren ta'addanci na neman zama ruwan dare, duk da ikirarin da gwamnatin mulkin sojin kasar ke yi na magance kalubane tsaro. Sabanin haka ma dai, bayanan masu karo da juna na yawo a shafukan sada zumunta kan halin da kauyen Barsalogho da ma yankin ke ciki. Amma wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewar an rufe kasuwar Kaya domin bai wa iyalai da ke bakin ciki damar binne ‘yan uwansu. Sai dai saboda tsoron kada a sace su don neman kudin fansa ko kuma a danganta su da wadanda suke hada kai da 'yan ta'adda, wasu mazauna na nema a sakaye sunnansu idan suka yi hira da manema labarai. Abin da ke faruwa ga wannan mazaunin garin Kaya ke nan

Karin Bayani: Burkina Faso: Damuwa kan kashe fararen hula

Yan Burkina Faso na zaman makokiHoto: Ingebjørg Kårstad/NRC

"Gaskiya wannan abu ne mai wuyar jurewa, harin ya yi min zafi sosai kuma haka abin ya ke kuma ake ji a Barsalogo, abin mamaki ne amma ba za mu bayar da kai domin bori ya hau ba. Abu ne mai sarkakiya, ka ga tsakanin Kaya da kauyen Barsalogo kilomita 40 ne kawai ya raba kuma ba za mu iya tashi daga Barsalogo mu nufi Kaya ba tare da rakiya ba."

Kusan sa'o'i takwas 'yan bindiga suka shafe suna kai wannan hari, kamar yadda wasu bayanai da ke yawo a shafukan sada zumunta suka nuna. Amma dai sanarwar da hukumar leken asirin Burkina Faso ta tabbatar da labarin harin na Barsalogo, wanda ke nuni da cewa an yi asarar rayuka da dama tare da raunata kusan mutane 200. Sannan 'yan ta'addan sun dauke motar jigilar sojoji da motar daukar marasa lafiya ta sojoji.

Mazaunin Kaya da bai so a bayyana sunansa ba ya kwatanta yanayin zaman dar-dar da ake ciki da wani abu na tashin hankali.

Karin Bayani: 'Yan ta'adda sun kona ofishin likitocin agaji a Burkina Faso

Wasu sojoji biyu a cikin wani choci a garin Kaya a Burkina Faso don nuna alhiniHoto: Sophie Garcia/AP/picture alliance

"Idan ka kira wani dan uwa a garin Barsalogo, sai ya zama ana zargin ka da marar hannu a hari ko abu mai kama da haka, don haka idan sojoji suka yi bincike kuma suka tabbatar da kiran da aka yi, kuma idan aka ce ka tuntubi wani, sai a dauke ka a matsayin wanda yake da alaka da 'yan ta'adda. Abu ne mai rikitarwa. Ina da abokai da yawa a Barsalogo da ba na kiran su saboda halin da ake ciki. Kuma iyalan da suka rasa dangi a garin Kaya da muka kai wa ziyara suna dimauce"

A wani mataki na taimakon kai da kai, wasu 'yan Burkina Faso na ba da gudunmawar jini don saukake kulawar wadanda suka ji rauni wadanda za a kwashe daga Barsalogo zuwa asibitin kwararru. Hare-haren ta'addanci na ci gaba da yin barna a Burkina Faso yayin da sojojin kasar suka ce suna ci gaba da aikin neman kwato yankunan kasar da ke hannun 'yan bindiga.