1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar taron dangi a yaki da ta'addanci

Gazali Abdou Tasawa
May 16, 2019

Kasar Burkina Faso ta yi kira ga kasashen duniya da su tashi tsaye wajen kafa wata rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa domin yakar matsalar ta'addancin da ta gagari kasashen Sahel. 

Nigrischer Soldat
Hoto: picture-alliance/Zumapress

Ministan harakokin wajen kasar ta Burkina Faso Alpha Barry ne ya sanya wannan kira a taron da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan Alhamis kan halin da ake ciki a yankin na Sahel. 

Minista Barry wanda ke magana da yawan kungiyar G5 Sahel a wurin wannan taro ya ce lokaci ya yi da ya kamata kasashen duniya su tashi su dauki mataki a yankin na Sahel kamar irin wanda suka dauka a Iraki da kuma Afganistan.

 Ministan wanda ya zano jerin hare-haren da kungiyoyin 'yan ta'adda suka kaddamar a baya baya bayan nan a Burkina Faso da kuma Nijar ya fito fili ya shaida wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya cewa matsalar ta'addancin da ake fuskanta a yankin ta fi karfin kasashen kungiyar ta G5 Sahel kuna tana bukatar taron dangi.