1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta samu nasara a kan 'yan ta'adda

Mouhamadou Awal Balarabe
May 11, 2021

Rundunar sojin Burkina Faso ta bayyana cewa ta kashe 'yan ta'adda akalla 20 tare da rusa sansanoninsu guda hudu, a lokacin da ta kai musu farmaki a arewacin kasar.

Burkina Faso | Übung Truppen aus Afrika
Hoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/D. White

Tun dai a  ranar 5 ga wata na Mayu ne, gwamnatin Burkina Faso ta kaddamar da wani gagarumin aikin na fatattakar kungiyoyin 'yan ta'adda da ke hana ruwa gudu a yakin sahel. Amma wannan dai ba shi ne karon farko da take sa kafar wando guda da 'yan bindiga ba, Sai dai har yanzu jami'an tsaron sun gaza kawo karshen tashin hankali da ake fama da shi a kasar. Ko a ranar Asabar da ta gabata, an kashe fararen hula uku a yankin arewacin Burkina Faso..
 
Burkina Faso da ke yammacin Afirka ta shafe sama da shekaru biyar tana fuskantar hare-hare masu muni, wadanda ake dangantawa da kungiyoyin masu da'awar jihadi. kimanin mutane 1,300 ne aka kashe a kasar tun daga 2015 yayin da aka tilasta wa mutane fiye da miliyan daya kaurace wa gidajensu.