An halaka fararan hula da dama a Burkina faso
October 28, 2019Rahotanni daga Burkina Faso na cewa akalla fararan hula 15 ne suka halaka a cikin jerin wasu hare-hare da wasu mutane dauke da makamai suka kaddamar a daren Asabar washe garin Lahadin da ta gabata a garin Pobe-Mengao na Jihar Soum da ke arewacin kasar, lamarin da ya tilasta wa mutanen garin tserewa zuwa birnin Djibo babban birnin jihar da ke a nisan kilomita 25.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wasu majiyoyi daga yankin na cewa an gano gawarwakin mutane 11 a safiyar jiya Lahadi kan hanyar da ke tashi daga birnin Pobe-Mengao zuwa Petelbongo, gawarwakin da ake kyautata zaton na mutanen garin na Pobe-Mengao ne da mayakan 'yan ta'adda suka sato a lokacin harin da suka kaddamar.
An kuma tsinto gawarwakin wasu mutanen hudu na daban, biyo bayan hari na biyu da 'yan bindigan suka kai a dai wannan dare a garin na Pobe-Mengao.