Burtaniya: Alhinin kamuwa da cutar daji da Kate ta yi
March 23, 2024Sanarwar da aka fitar ya sanya shakku da kuma damuwa kan yadda manyan masu rike da sarautar Burtaniya ke fama da cutar daji. Watanni 17 da hawa kan gadon sarautar Burtaniya, fadar Burkingham ta sanar da cewa Sarki Charles III na dauke da cutar daji wanda hakan ya sanya soke dukkan wasu muhimman ayyukan da Sarkin ke gudanarwa.
Karin bayani: Auren Yarima William
Jaridun Burtaniya sun rawaito Firaiministan kasar Rishi Sunak da fadar White House na Amurka sun yi jinjina ga gimbiya Kate juriyar da ta nuna kamar yadda kalaman su suka mamaye shafukan jaridun Burtaniya dauke da hoton Gimbiya Kate.
Karin bayani: Sarki Charles III ya yi alkawarin koyi da mahaifiyarsa
A jawabin da ta wallafa a shafinta na X Gimbiya Kate ta ce ta kadu matuka bayan likitoci sun sanar da ita cewa tana dauke da cutar Cancer, bayan an dauki tsawon lokaci ana gudanar da bincike.