1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelensky na ziyara a birnin Landon

March 17, 2026

Zelensky na ziyara a birnin Landon domin ganawa da firaministan Burtaniya da sakataren kungiyar tsaro ta NATO da kuma Sarki Charls III.

Firaministan Burtaniya da shugaban kasar Ukraine
Firaministan Burtaniya da shugaban kasar Ukraine Hoto: Henry Nicholls/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya isa birnin Landon domin ganawa da Firaministan Birtaniya Keir Starmer da kuma Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte, kamar yadda kakakin fadar mulki ta Kiev ya sanar a Talatar nan.

Gabanin wannan sanarwa, fadar mulki ta Downing Street ta bayyana cewa Burtaniya da Ukraine na shirin rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro, wadda za ta mayar da hankali musamman kan dabarun dakile barazanar jiragen yaki marasa matuka.

Ana kuma sa ran Zelensky zai gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham sannan zai gabatar da jawabi a gaban 'yan majalisar dokokin Burtaniya kafin daga bisani ya daga zuwa Spain a ranar Laraba.

Wannan ziyarar ta Zelensky na zuwa ne a daidai lokacin da yakin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya ya dakatar da kokarin diflomasiyya da Amurka ke jagoranta na neman kawo karshen rikicin Ukraine da Rasha wanda ya shafe sama da shekaru hudu.