Burtaniya ta amince da Falasdinu a matsayin kasa
September 21, 2025
Firaministan Burtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa daga wannan Lahadi, a hukumance kasarsa ta amince da kasar Falasdinu. Wannan mataki ya saba wa tsohuwar matsayar Burtaniya, wadda ke cewa dole a jira a ga yadda tattaunawar tsagaita wuta ta kaya a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas kafin amince da Falasdinun a matsayin kasa.
A watan Yuli, Mr. Starmer ya gargadi Isra'ila cewa Burtaniya za ta goyi bayan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya idan Isra'ilan ba ta dauki matakin dakatar da rikicin Gaza ba. Wannan mataki ya sanya Burtaniya cikin jerin kasashe fiye da 140 da suka amince da Falasdinu.
Kasashen Ostireliya da Kanada su ma sun amince da Falasdinun a matsayin kasa, inda firaminista Anthony Albanese na Ostireliya, da na Kanada, Mark Carney, suka ce hakan wani yunkuri ne na hadin gwiwa don farfado da mafita ta samar da kasashe biyu.
Karin bayani: Canada za ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce zai ci gaba da adawa da wannan mataki, yana mai cewa kafa kasar Falasdinu zai kawo barazana ga Isra'ila.