1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Burtaniya ta nuna damuwa game da tashin hankali a Pakistan

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 9, 2024

Rundunar 'yan sandan Pakistan ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a juma'ar nan, bayan arangama da 'yan sandan suka yi da magoya bayan tsohon firaministan kasar da ke tsare Imran Khan

Hoto: Banaras Khan/AFP/Getty Images

Burtaniya ta nuna damuwa matuka game da halin da ake ciki na tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Pakistan a dalilin babban zaben kasar da aka gudanar.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya David Cameron ya ce kasarsa ta damu sosai game da ingancin zaben la'akari da irin rashin adalcin da ake nunawa wasu jam'iyyu na hana su shiga zaben ta hanyar amfani da bangaren shari'ar kasar.

Karin bayani:Harin ta'addanci a Pakistan ya halaka mutane kusan 30

Tsohon firaministan kasar Imran Khan da yanzu haka ke kurkuku, na daga cikin wadanda aka haramtawa shiga zaben, inda magoya bayansa ke ci gaba da yin fito-na-fito da hukumomin Pakistan din.

Rundunar 'yan sandan Pakistan ta tabbatar da mutuwar mutane biyu yau juma'a, bayan arangama da 'yan sandan suka yi da magoya bayan tsohon firaministan kasar da ke tsare Imran Khan.

Karin bayani:Ana gudanar da zabe a kasar Pakistan

Wani jami'in 'dan sanda a yankin Shangla da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa mai suna Sahibzada Sajjad Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa magoya bayan Imran Khan da ke zanga-zanga, sun rinka jifan 'yan sandan da duwatsu, a wannan artabu ne kuma biyu daga cikinsu suka rasu.

Tuni dai ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta sanar da katse layukan waya baki-daya, don ganin ta dawo da doka da oda, amma ba ta yi karin haske kan ko zuwa wane lokaci za a dawo da layukan ba, Inda kuma ake sa ran fitar da sakamakon zaben a juma'ar nan.