Burtaniya ta rushe shirin tura 'yan gudun hijira Rwanda
July 6, 2024Sabon firaministan Burtaniya Keir Starmer, ya sanar da rushe shirin aike wa da masu neman mafaka a Burntaniya zuwa Rwanda da gwamnatin baya ta Rishi Sunak ta kaddamar.
Karin bayani:Birtaniya: Sabon firaminista ya kama aiki
Wannan sanarwa ta Mr Starmer a Asabar din nan, da ke zama cikakkiyar rana ta farko da ya fara aikinsa a matsayinsa na firaministan Burtaniya, ta zo ne bayan gagarumar nasarar da jam'iyyarsa ta Labour ta samu, wajen kayar da mai rike da iko ta tsohon firaminista Rishi Sunak wato Conservative, wadda ta shafe shekaru 14 tana mulki.
Karin bayani:Burtaniya ta kafe kan bakanta na aikewa da 'yan gudun hijirar cikin kasar zuwa Rwanda
Starmer ya shaidawa manema labarai a fadarsa ta Number 10 Downing street cewa baya goyon wannan tsari da ya kira dodorido, wanda ba zai taba zama izina ga masu yunkurin shiga Burtaniya ta barauniyar hanya ba, kuma gwamnatinsa za ta jajirce wajen ciyar da Burtaniya gaba.