1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burtaniya ta saka takunkumi ga masu tallafa wa rikicin Sudan

April 15, 2024

Burtaniya ta sanar da saka takunkumai ga masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa rikicin Sudan da ake gwabzawa tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar, da ya cika shekara guda da barkewa a ranar 15.04.2024.

Burtaniya ta saka takunkumi ga masu tallafa wa rikicin Sudan
Burtaniya ta saka takunkumi ga masu tallafa wa rikicin SudanHoto: Mohamed Babiker/Photoshot/picture alliance

A cikin sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta fidda ta ce takunkuman sun jibanci kwace kudaden wani Bankin Sudan da ake kira Alkhaleej wanda ta bayyana a matsayin mai samar da kudade ga dakarun kar ta kwana na RSF na Mohammed Hamdan Dagalo, da kuma kamfanin Al-Fakher Advanced Work wanda ke taimaka musu wajen fitar da zinariya daga kasar.

Kazalika takunkuman na London sun shafi kamfanin Red Rock Mining wanda shi kuma ke zama kirjin samar da kudi da dakarun gwamnatin rikon kwarya ta Abdel Fatah ll Burhane.

Karin bayani: Amurka na shirin kawo karshen yakin Sudan

Wannan sanarwa ta David Cameron na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin agagi na kasa da kasa ke taron a birnin Paris karshashin Faransa da Jamus da kuma Tarayyar Turai da nufin samar da kudade don tallafa wa wadanda rikicin na Sudan ya jefa cikin kuncin rayuwa da yawansu ya kai mutum miliyan 25.

Karin bayani: Mutum miliyan biyar na cikin barazanar yunwa a Sudan - MDD

Tuni bayan dube wannan taron aka yi nasarar tattara kudade da suka kai miliyan 840 na Yuro domin gudanar da tsare-tsare na inganta rayuwar al'ummar Sudan da rikicin da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilun bara ya daidaita.