1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Doka da odaRuwanda

Burtaniya ta yi nasara kan Rwanda a Kotu

Abdullahi Tanko Bala
June 1, 2026

Kotun kasa da kasa da ke Hague ta yi wasti da daukaka karar da Rwanda ta yi na neman diyya bayan soke shirin tura masu neman mafaka zuwa kasar ta gabashin Afirka.

Tsohon Firaministan Burtaniya Rishi Sunak a tashar ruwan Dova
Tsohon Firaministan Burtaniya Rishi Sunak a tashar ruwan DovaHoto: Yui Mok/empics/picture alliance

Kasar ta Rwanda ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da tsohuwar gwamnatin Burtaniya wadda Firaminista na yanzu Keir Starmer ya soke bayan da ya hau karagar mulki a 2024.

A karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka sanya wa hannu, yan gudun hijira da suka shiga Burtaniya ta barauniyar hanya  za a tasa keyarsu zuwa Rwanda inda daga nan za su rubuta takardar neman mafaka ko zama na dundundun a hukumance.

Sai dai gwamnatin da ta zo daga baya ta baiyana tsarin a matsayin wani choge kuma barnar dukiyar al'umma inda Firaministan Starmer yace Burtaniya ta biya biliyoyin kudade masu yawa a shirin da ba a zato zai wakana.