1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Evariste Ndayishimiye ya zama shugaban kasa

Zainab Mohammed Abubakar
June 18, 2020

Evariste Ndayishimiye ya sha rantsuwar hawa karagar shugabanci, watanni biyu kafin lokaci biyo bayan mutuwar ba-zatan tsohon shugaba Pierre Nkurunziza.

Burundi Vereidigung Präsident Evariste Ndayishimiye
Hoto: Getty Images/AFP/T. Nitanga

Mai shekaru 52 da haihuwa Ndayishimiye, da ke zama tsohon janar na rundunar soji, shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a watan da ya gabata, a karkashin tutar jam'iyya mai mulki, inda ya doke Agathon Rwasa na bangaren adawa da wasu 'yan takara biyar.

Mutuwar tsohon shugaba Nkurunziza da ke shirin ajiye mulki a watan Augusta bayan shekaru 15, ya bar wannan kasar ta yankin gabashin Afirka cikin rudanin rashin sanin makoma.

Daga bisani Kotun tsarin mulkin kasar ta umurci ministocin Burundin da su rantsar da shugaba mai jiran gadon. 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW