1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBurundi

Bunyoni na Burundi zai fuskanci hukunci

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 8, 2023

Kotun kolin Burundi ta samu tsohon firamnistan kasar Alain-Guillaume Bunyoni da laifin yunkurin kifar da gwamnati da kuma yin barazana ga rayuwar shugaban kasa.

Burundi | Hukunci | Alain Guillaume Bunyoni
Tsohon firamnistan Burundi Alain-Guillaume Bunyoni Hoto: Guven Yilmaz/AA/picture alliance/dpa

Kotun kolin Burundin dai ta ce wadannan laifuka da aka samu tsohon firamnistan Alain-Guillaume Bunyoni shi da aikatawa ne, suka sanya  ta yanke masa hukuncin daurin na rai-da-rai. Majiyoyin shari'ar kasar dai, sun tabbatar da da wannan batu na hukuncin zargi kan juyin mulkinga tsohon firamnistan Alain-Guillaume Bunyoni. A watannin da suka gabata ne aka fara shari'ar ta Bunyoni wanda ya rike mukamin firamnista tsakanin shekara ta 2020 zuwa 2022, kafin a sauke shi daga mukaminsa bayan da Shugaba Evariste Ndayishimiye ya yi zargin an yi masa yunkurin juyin mulki.