Shirin zaben raba gardama a Burundi
May 15, 2018Talla
'Yan Burundi kimanin miliyan hudu da dubu dari takwas ne za su yi zaben kwatankwacin kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar da suka yi rajista, inda za su zabi amincewa ko kuma akasin haka da sauye-sauyen kudin tsarin mulkin kasar.
Tun bayan da Shugaban Nkurunziza ya sake tsayawa takara mai cike da cece kuce a shekarar 2015 wanda ake kallo a matsayin wani wa'adin mulki na uku, lamarin ya jefa kasar ta Burundi cikin tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 1, 200 yayin da wasu sama da dubu 400 suka kasance 'yan gudun hijira.