Burundi: Soke kungiyar kare hakin dan Adam ta Iteka
January 3, 2017Talla
Wannan kungiya ta Iteka da ke nufin diyauci a harshen Kirundi na kasar ta Burundi, an kafata ne tun a shekara ta 1991, kuma aka dakatar da ita tun farkon rikicin siyasar da ya barke a watan Afrilu na 2015, lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsawa takarar neman shugabncin kasar ta Burundi a lokacin da ake kallon cewa wa'adin mulkinsa ya kawo karshe.
Wannan mataki dai ya biyo bayan wani rahoto da kungiyar ta fitar tare da hadin gwiwar kungiyar kare hakin dan Adam ta duniya da kungiyar ta Iteka ke wakilta a kasar ta Burundi, kan iri-irin cin zarafin da ke gudana a kasar. Sai dai hukumomin na Burundin na zargin wannan kungiya da ci gaba da bata sunan kasar a idanun duniya.