Burundi ta amince da dakarun Majalisar Dinkin Duniya
April 3, 2016Talla
Ministan harkokin wajen kasar ta Burundi ne dai Alain Nyamitwe ya sanar da amincewar kasar, abun da ya kawo karshen ja in ja din da aka dade ana yi tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin ta Shugaba Pierre Nkurunziza.
Gabaki daya dai membobi 15 na Kwamitin Sulhun ne suka amince da wannan mataki da kasar Faransa ta gabatar, inda ta nemi da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya gabatar da tsare-tsaran isar da jami'an tsaro na 'yan sanda a karkashin inuwar ta MDD domin taimaka wa wajan samar da tsaro a kasar da ke daf da fadawa cikin wani sabon rikicin kabilanci.