1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta kada kuri'ar raba gari da ICC

October 14, 2016

A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ya shirya tura wakili da zai shiga tsakani a rikicin Burundi, 'yan majalisa da ke goyon bayan shugaba Nkurunziza sun amince da kudirin doka da zai yanke hulda da kotun ICC.

Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Bayan da a a ranar Laraba suka zauna kan kudurin dokar yanke hulda da kotun ta ICC, mambobin majalisar 94 daga cikin 110 sun amince da kudirin dokar, biyu suka nuna tirjiya, 14 ba su halarci zaman majalisar ba. Zenon Ndaruvukanye na daga cikin 'yan majalisar da suka goyi bayan janyewar. Ya ce " Al'ummomi na kasa da kasa son shirya ne su rusa kasar ta Burundi duk da kokarin da mahukunta ke yi na ganin dimukaradiyya ta girku, a matsayina na dan majalisa ina ganin janyewa daga kotun ya yi daidai saboda ICC na daurewa masu laifi gindi tana tozarta wadanda ke son ganin kasashensu sun ci gaba.

 

Andre Ndayizamba, wani dan majalisar kuwa na ganin janyewa daga kotun ta ICC babban kuskure ne ta fiskar diplomasiya da ma siyasa. Ya ce " kotun a waje na ba ta da wata matsala, amma mu a nan Afirka ba mu yi wani nisa ba kan batun kare hakkin bil Adama, anan ne zaka ga gwamnati na kashe al'ummata da kanta ga wasu kuwa ko da za su yi ta'asar ne a wajen kasarsuamma nan Afirka mukan yi ne a gida.

Da dama dai na ganin wannan kotu a matsayin wacce ta maida hankali kan nahiyar ta Afirka inda ta ke farautar shugabanni daga Afirka, sai dai wadannan al'umma a birnin Bujumbura na da ra'ayoyi mabambanta. Wannan mutumin na cewa: " Burundi ta makara dan wannan kotu na gallazawa ne ga kasashe masu talauci dan su ke korafi cewa kotun ICC ana amfani da ita dan kawai a gallazawa wasu.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Lampen

Sai dai wannan dan Burundi bai yarda da wannan ra'ayi ba, inda ya ce " Ina ganin wannan ba daidai ba ne a kasar Burundi inda ake take hakkin bil Adama a lokuta da dama, wadanda suka yi laifiin ba a hukuntasu. Kamata ya yi Burundi ta ci gaba da zama cikin wadanda ke bin kotun ta ICC dan ganin mutanen da aka ci zarafinsu a bi musu hakki.


Tuni dai Ban Ki-moon ya bukaci mahukuntan kasar su janye wannan mataki, sannan jakadan Majalisar Dinkin Duniya Jamal Benomar  zai je kasar ta Burundi a mako mai zuwa don tattaunawa da mahukuntan kasar  kan rikicin da ke faruwa da ma batun yanke hulda da jami'an hukumar kare hakkin bil dama daga majalisar abin da ke zuwa daidai lokacin da kasar ke sake nuna tirjiya ga kai jami'an tsaro kasar daga MDD.

Fiye da mutane 500 ne dai suka rasu kusan 300,000 suka kaurace wa muhallansu tun bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi tazarce karo na uku.