1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta kori jami'an hukumar lafiya WHO

Abdullahi Tanko Bala
May 14, 2020

Kasar Burundi ta kori wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO tare da wasu jami'an hukumar su uku gabanin zaben shugaban kasar da ke tafe

Burundi | Wahlkampf | Wahlen | Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/Photoshot/E. Ngendakumana

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce jami'an suna zaman kansu ne a saboda haka ta umarcesu su hanzarta ficewa daga kasar ta gabashin Afirka zuwa rsnsr 15 ga watan Afrilu a cewar wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar Ezechiel Nibigira ya sanyawa hannu.

Daraktan hukumar lafiyar ta duniya mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti ta ce suna tuntubar hukumomin na Burundi domin tantance dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki.

A ranar 20 ga watan Mayu Burundi za ta gudanar da zaben shugaban kasa yayin da ake tsakiyar annobar corona domin zaben shugaban kasa da zai maye gurbin shugaba Pierre Nkurunziza.

Hukumar lafiyar ta duniya ta ce idan har za a gudanar da zabe a tsakiyar annoba to wajibi ne a yi hakan bisa tsauraran dokoki na matakan lafiya.