1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Evariste Ndayishimiye ya lashe zaben Burundi

Gazali Abdou Tasawa
May 26, 2020

Tuni dan takarar adawa Agathon Rwasa ya sanar da shirin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar a gaban kotun tsarin mulkin kasar.

Burundi Präsidentschaftswahl Evariste Ndayishimiye
Hoto: Reuters/E. Ngendakumana

Sakamakon wucin gadin wanda hukumar zaben kasar ta Burundi ta bayyana a ranar Litinin ya nunar da cewa dan takarar jam'iyya mai mulki ta CNDD-FDD wato Evariste Ndayishimiye a zaben shugaban kasar shi ne ya lashe zaben da kaso 68,72 cikin dari a yayin da abokin hamayyarsa na bangaren adawa Agathon Rwasa ya samu kaso 24,19 cikin dari. Sai dai 'yan adawar kasar ta Burundi wadanda suka jima suna hankoran samar da sauyi a kasar sun bayyana nasarar ta Ndayishimiye na hannun damar Shugaba Pierre Nkurunziza a matsayin wani dodoridon siyasa kawai. Kuma Pancras Cimpaye daya daga cikin 'yan adawar kasar ta Burundi  da ke zaman gudun hijira a Beljiyam, bayyana sakamakon zaben ya yi da juyin mulki kawai: '' Wannan juyin mulki ne kawai aka yi wa zabin al'umma wacce ta fito dafifi ta kawo goyon bayanta ga tawagar 'yan canji a karkashin jagorancin Agathon Rwasa. Don haka mu a wurinmu murdiya ce kawai aka yi ba wani abu ba."

Martanin gwamnatin Burundi a game da korafin 'yan adawar

Pierre Nkurunziza shugaba mai barin gado na BurundiHoto: Reuters/E. Ngendakumana

Da yake mayar da martani kan korafin 'yan adawar, jakadan kasar Burundi a MDD Ambasada Albert Shingiro cewa ya yi korafin 'yan adawar kasar ta Burundi ba bako ba ne ba domin shekaru da dama ke'nan da gatanar gizo ta kasa wuce koki inda suke musanta sakamakon a duk lokacin da suka sha kayi a akwatinan zabe inda ya yi karin bayani yana mai cewa: ''Wakar tasu kullum irin daya ce. Dan takarar da ake magana kansa, mutum ne da yake yin watsi da sakamakon zabe tun a shekara ta 2010. Amma ina fatan a wannan karon zai yi wa kansa kiyamun laili domin zaben ya gudana cikin adalci kuma an wallafa sakamakon zaben kai tsaye a shafukan Intanet a bisa idon kafafan yada labarai." Babbar jam'iyyar adawa ta Agathon Rwasa dai ta yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayyana, sannan ya sanar da shirin kalubalantarsa a gaban kotun tsarin mulkin kasar duk da kallon da yake yi wa kotun na kasancewa 'yar amshin shatar gwamnati.

'Yan adawa na Burundi a Beljiyam sun ce babu amfanin shigar da kara 

Hoto: DW/A. Niragira

Pancras Cimpaye dan adawar kasar ta Burundi da ke zaman gudun hijira a Brussels ya ce zai wuya koken 'yan adawar ya kai labari a gaban kotun tsarin mulkin kasar, don haka ya ce hanya daya wajen tilasta canji a kasar shi ne 'yan adawa su hada kai waje daya domin ceto al'ummar kasar daga mulkin danniyar da aka share shekaru ana yi mata: '' Ya zama dole ga adawa da ta tashi tsaye ta kwato wa al'umma 'yancinta domin kaucewa azabtarwa, kisa da tilasta wa al'umma shiga hijira. Domin haka a yau ya kamata 'yan adawa su kawo karshen rarrabuwar kawunan da zaman 'yan marina da suke yi da lissafin duna domin jibintar bukatun al'umma domin tinkarar wannan mulki" Tuni dai Shugaba Nkurunziza ya yi wa sabon shugaban barka da lashe zabe. 'Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga ko dan takarar adawar ya shigar da karar a gaban kotun tsarin mulkin kamar yadda ya yi alkawari. A watan Agusta mai zuwa ne dai za a rantsar da sabon shugaban kasar ta Burundi a wani sabon wa'adi na tsawon shekaru bakwai da zai kawo karshen mulkin shugaba Pierre Nkurunziza.