1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun AU ta amince da takarar Laurent Gbagbo

September 26, 2020

Kotun kare hakkin dan Adam ta tarayyar Afirka, ta umurci hukumomin Côte d'Ivoire  su sanya tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo cikin 'yan takarar zaben shugaban kasa na watan Oktoba.

Elfenbeinküste Laurent Gbagbo wird als Präsident vereidigt
Hoto: picture-alliance/epa/L. Koula

Hukuncin kotun na ranar Jumma'a na  zuwa ne bayan da kotun tsarin mulkin kasar Côte d'Ivoire ta cire sunan Laurent Gbagbo din daga cikin wadanda za su tsaya takara bisa hujjar cewa a watan Nuwambar da ya gabata wata kotu a kasar ta yanke masa hukuncin zaman shekaru 20 a gidan yari biyo bayan samunsa da laifin kwashe dukiyar kasar a a zamanin mulkinsa. To amma  Gbagbo wanda yanzu haka ke zaune a birnin Brussels na Beljiyum ya kafe kai-da-fata cewa ya cancanci sake jagorantar kasar ta Côte d'Ivoire

Tsohon shugaban dai ya mulki Côte d'Ivoire a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2010 lokacin da ya ki amincewa da kayan da shugaba mai ci Alassane Ouattara ya yi masa, lamarin da ya haifar da tashin hankalin da ya kashe mutum 3,000. Da farko an garkame shi amma kuma a shekarar a bara kotun manyan laifuka ta duniya ta wanke Gbagbo daga zarginsa da hannu a kisan kare dangi.