1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cacar-baka a tsakanin Rasha da kasashen yamma

Ramatu Garba Baba
February 19, 2023

Rasha ta zargi manyan kasashen yamma da yawan surutu a maimakon mayar da hankali kan samar da maslaha daga yakin da take da Ukraine.

Mahalarta taro kan tsaro a birnin Munich
Mahalarta taro kan tsaro a birnin MunichHoto: Azerbaijani Presidency /AA/picture alliance

Fadar Kremlin ta ce, har yanzu kasashen yammacin duniya ba su fito sun nuna a fili ko kuma a aikace cewar, a shirye suke su shiga zaman warware rikicinta da Ukraine ba. Kakakin fadar Dmitry Peskov ne ya sheda haka yana mai cewa, a aikace dai, babu wani shiri ko kafar zaman lafiya da hadakar kasashen yamma ta samar da ke nuna alamun a yi sassanci.

A yayin rufe taro kan tsaro da ya gudana a birnin Munich na Jamus, Amurka ta ci gaba da yin gargadi ga Chaina a game da shirinta na taimaka wa Rasha da duk wani nau'in taimako a yakin da take a Ukraine, lamarin da Amurkan ta ce, zai haifar da matsala babba a dangantakar kasashen biyu.