Cacar baka tsakanin Italiya da Brazil
December 31, 2010Ƙasashen Italiya da Brazil sun shiga wata cacar baka, sakamakon matakin da shugaba Lula Da Silva mai barin gado, ya ɗauka na ƙin miƙa Cesare Battisti, wani ɗan Italiya da hukumomin ƙasar ke nema ruwa jallo, wanda kuma a halin yanzu ya fake a Brazil.
Hukumomin Italiya na bukatar gurfanar da Battisti gaban kuliya bayan zargin da su ka yi masa na aikata kisan gilla.
To sai dai shugaba Luiz Inacio Lula Da Silva da zai sauka daga karagar mulkin Brazil a yau Juma´a, ya ce ba zai miƙa kai ba, game da wannan bukata, domin akwai zullumin nuna rashin adalci ga Cesare Battisti, wanda ya musanta zargin da ake yi masa.
Don nuna ɓacin rai game da wannan mataki, Silvio Berlusconi ya kiri jakadan Italiya a ƙasar Brazil.
Dukan ɓangarorin siyasar Italiya na adawa da masu mulki, sun yi Allah wadai da matakin na Brazil, tare da danganta Lula Da Silva da haɗin kai ga dan ta´adda.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal