1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Tsare dan leken asirin Rasha

December 26, 2022

Hukumar Leken Asiri ta Tarayyar Jamus ta bankado wani da ake zargin dan leken asirin Rasha ne, inda yanzu haka ake tsare da shi.

Jamus | Hukumar Leken Asiri | Bruno Kahl
Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Jamus Bruno KahlHoto: Fabian Sommer/dpa/picture alliance

Wata kotun a garin Karlsruhe na Jamus din, ta ce mutumin mai sunan Carsten L da ya kasance ma'aikaci ne a Hukumar Leken Asirin ta Tarayyar Jamusta BND, ya bayar da bayanai da aka tattara a matsayin wani bangare na aikinsa ga Ma'aikatar Leken Asirin Rasha a wannan shekara da muke ciki ta 2022. Shugaban Hukumar Leken Asiri na Jamus na BND Bruno Kahl ya bayyana cewa, Rasha a shirye take ta wargaza duniya. Tun a tsakiyar watan Oktoba, shugaban na hukumar BND ya ambata a fili game da shugaban Kremlin Vladimir Putin cewa, zai ci gaba da amfani da tashin hankali domin cimma burinsa na siyasa.

Hukumar Leken Asiri ta Jamus ta cafke wani jami'intaHoto: Joko/imageBROKER/picture alliance

Manufar Rasha ita ce ta tattara bayanai na sirri da yawa gwargwadon iko kan hanyoyin dabarun Jamus, musamman makamashi da hanyoyin kimiyya da fasaha. Manyan kamfanonin Jamus ma suna cikin tsaka-mai-wuya, kan barazanar leken asirin fasaha. Tun bayan da aka fara yakin Ukraine ayyukan leken asirin Rasha a Jamus suka karu fiye da yadda ake tsamanin, abin da ke zama babbar barazana. Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka kama jami'in Hukumar Leken Asirin ta Jamusta BND da laifin yi wa wata kasa leken asiri ba, ko a shekara ta 2016 hukumar ta cafke wani jam'in da ya rika yi wa Amirka leken asiri tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru takwas na gidan kaso.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani