1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke matan Afirka da ke karuwanci a Spain

June 2, 2013

Jami'an 'yan sanda a kasar Spain sun cafke wasu mutane da ke yin safarar mata daga Najeriya domin sa su karuwanci.

#23042080 - Reeperbahn Hamburg © ts-grafik.de - Fotolia.com
Schild Sex über dem Eingang eines SexshopsHoto: Fotolia/ts-grafik.de

'Yan sandan sun cafke muatane su shida 'yan asalin Najeriya da suke zargi da karuwanci  tare da shugabarsu, a wani bangare na binciken da suka kaddamar a bara bayan da daya daga cikin matan da ake tilastawa yin karuwancin ta kai korafi ga hukumomi.

Rahotanni sun bayyana cewa mafi yawan matan ana dauko su  ne daga garin Benin na Najeriya tare da tilasta musu yin karuwanci ta hanyar azabtar da su da wuta da kuma tsafi, kuma da yawa daga cikinsu mazajensu da kuma iyayensu sun mutu-dalilin da yasa suke farautar abin da za su ciyar da 'ya'yansu.

Mawallafiya: Lateefa Mutapha Ja'Afar
Edita:Halima Balaraba Abbas