1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jamus ta soki China kan kame a yankin Hong Kong

Suleiman Babayo AH
January 6, 2021

Jamus ta nuna damuwa bisa matakin mahukuntan China na ci gaba da cafke 'yan gwagwarmaya da ke neman tabbatar da tsarin dimukaradiyya a yankin Hong Kong na kasar.

Symbolbild | Protest | Rund 50 prodemokratische Aktivisten in Hongkong festgenommen
Hoto: May James/AFP

Ministan harkokin wajen kasar Jamus, Heiko Maas, ya ce cafke masu raji demokuradiyya fiye da 50 a yankin Hong Kong na tabbatar da tsaron da Jamus take nunawa kan mahukuntan China na amfani da dokar tsaron kasa domin hana fadin albarkacin baki, a samame mafi girma da aka fuskanta tun lokacin da China ta fara aiki da dokokin tsaro a yankin a shekarar da ta gabata.

Ministan ya ce China tana kara kaucewa daga alkawarin da ta yi wa kasashen duniya lokacin da yankin Hong Kong ya koma karkashin ikon kasar, bisa amincewa yankin zai ci gaba da aikin da dokokinsa.